Boko haram: Mubi ta koma 'Madinatul Islam'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta fara kaddamar da shari'ar musulinci a Mubi, a cewar mazauna garin.

Kungiyar Boko Haram da ta kwace garin Mubi na jihar Adamawa a Nigeria ta sauya sunan garin zuwa "madinatul Islam", watau birnin musulinci.

Mazauna garin sun ce 'yan kungiyar sun fara yin amfani da dokokin addinin musulinci.

Wani mazauni garin ya shaida wa BBC cewa 'yan kungiyar sun yanke hukuncin kisa kan mutanen da aka kama da liafin yin sata.

A makon jiya ne dai 'yan Boko Haram suka fatattaki sojoji daga garin, sannan suka kwace shi.

Karin bayani