Ebola: An kama dan jarida a Saliyau

Cutar Ebola Hakkin mallakar hoto

An kama wani dan jarida a Saliyo saboda sukan shugaban kasar Ernest Bai Koroma da gwamnatinsa kan yadda suke tafiyar da yaki da cutar Ebola.

Dan jaridar, David Tam Baryoh, ya yi wata hira ne da wani mai magana da yawun 'yan adawa, wanda ya soki shugaban da jamiyya mai mulki.

Kungiyar kare 'yan jarida, ta, Committee to Protect Journalists, ta yi allawadai da kamun nasa.

A halin da ake ciki kuma sabuwar darektar Afrika da Hukumar Lafiya ta Duniya ta nada sakamakon sukar da ake yi wa hukumar kan yadda take sakaci da batun yaki da cutar Ebola, Dr Matshidiso Rebecca Mo├ęti 'yar Botswana, ta yi gargadi ga kasashen da cutar ta shafa da su zauna da shirin sake bullarta a gaba...........Clip

Ta ce, ''Dole ne mu yarda cewa, bayan wannan mummunar annoba, lamarin zai ci gaba da zama abin damuwa ga lafiyar jama'a, a yankin har zuwa wani lokaci, ko da kuwa an shawo kanta.''