An kama 'yan luwadi 25 a Kebbi

Image caption An haramta luwadi a Nigeria

Kungiyar 'yan sintiri a jihar Kebbi a Nigeria ta ce cikin shekaru guda ta cafke 'yan luwadi 25 a jihar wadanda ta mika su gaban kuliya.

Shugaban kungiyar, Sanusi Ibrahim Geza ya shaidawa BBC cewar wasu daga cikin 'yan luwadin har an yanke musu hukuncin dauri a gidan yari wasu kuma an yi musu bulala.

A cewarsa, kungiyar ta yi nasarar cafke masu aikata munanan laifuka a sassa daban-daban na jihar wadanda ta gabatar da su gaban shari'a.

Dokar Nigeria ta haramta luwadi kuma duk wanda aka kama da laifin hakan za su sha daurin a kalla shekaru 14 a gidan yari.