An kashe malamin addinin musulunci a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana takun tsakan tsakanin jami'an tsaro da malamai a Kenya

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun harbe wani fitaccen malamin addinin musulunci mai matsakaicin ra'ayi a Kenya.

An harbe Sheikh Salim Bakari Mwarangi, wanda mai rajin tabbatar da zaman lafiya ne da kuma adawa da tsattsauran ra'ayi, yayin da yake dawo wa gida daga masallaci bayan sallar Isha, a ranar Talata.

Kawo yanzu an kashe malaman addinin musulunci shida da suka kunshi masu tsattsauran ra'ayi da masu sassauci a birnin na Mombasa tun shekara ta 2012.

Yankin gabar tekun Kenya, wanda yake da dimbin al'ummar musulmi, yana fama da matsalar hare-haren bam, da ake dora alhakinsu akan kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Somalia al-Shabab.