Za a daukaka karar hukuncin Pistorius

Oscar Pistorius
Image caption Masu shigar da kara sun ce an yiwa Pistorius sassauci da yawa

Masu Shigar da kara a Afrika ta Kudu na neman iznin daukaka karar hukuncin da aka yankewa dan tseren nakasassu Oscar Pistorius.

A watan da ya gabata ne wata kotun kasar ta yankewa Pistorius hukuncin daurin shekara biyar bayan da aka same shi da laifin kashe budurwarsa Reeva Steenkamp.

Amma masu shigar da karar sun ce kotun ta yiwa Pistorius sassauci da yawa idan aka yi la'akkari da yadda ya aikata kisan.

"Kotun ba ta yi la'akkari da irin hanyar rashin tausayin da aka kashe Steenkamp ba." In ji daya daga cikin masu shigar da karar.