'Yan republican sun lashe zabe

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Yanzu haka ta tabbata cewa 'yan jam'iyyar Republican a kasar Amurka za su ci gaba da jagorancin majalisun dokokin kasar, bayan da suka lashe mafi yawan kujerun majalisun a zaben rabin wa'adi da aka gudanar.

'yan jamiyyar ta Republican dai sun lashe kujeru bakwai ne a majalisar dattawa wanda hakan ya wuce yawan kujerun da suke bukata na samun rinjaye a majalisun.

Har ila yau rahotanni na cewa shugaban Republican a majalisar Dattawa, Mitch McConnell ya sake samun nasarar rike kujerar sa a Jihar Kenturkey

Karin bayani