'Hotunan 3D za su iya bata idanun yara kanana'

3D Hakkin mallakar hoto video
Image caption Yara 'yan shekaru 13 ka iya fuskantar matsalar idanu suka yawaita kallon 3D

Wata hukumar kare lafiya mai zaman kanta ta ce hotunan bidiyo masu nau'in 3D kan iya yin illa ga idanun yara kanana.

A wani bincike da hukumar ANSES ta gudanar, ta ce yara dake da shekaru kasa da shida bai kamata sun dinga kallon hotunan bidiyo na 3D ba.

Su dai hotunan bidiyo na 3D kan bayar da bangarorin kallon ne fiye da daya a ababan kallo.

Kuma hakan na bukatar idanu sun dinga juyawa daga wannan bangaren zuwa wancan kamin mutum ya fahimci abin da yake kallo.

Hakan kuma a cewar hukumar bai kamaci idanuwan yara ba saboda suna kan girma ne.

A cewar hukumar tare da yin la'akkari da cewa lafiyar idanuwan yara na karuwa ne a hankali saboda karancin shekarunsu hakan zai iya sa hotunan 3D su zama cikas ga lafiyar idanun nasu.

Hukumar ta ANSES ta kara da cewa ya kamata yara masu shekaru 13 suma su yi taka tsan- tsan, wato abin nufi kada su cika kallon hotunan bidiyo na 3D.

Yanzu haka kasashe kadan a duniya ne ke da dokoki dake kare masu yin amfani da hotunan bidiyo na 3D.