Everton ta gyara zama a saman rukunin H

Everton
Image caption Everton ta shiga zagayen 'yan 32

Kungiyar Everton ta sake karfafa zamanta a saman rukunin H a gasar Europa League bayan da ta doke kungiyar Lille da ci 3-0.

Leon Osman da Phil Jagielka da kuma Steven Naismith ne suka zirawa Everton kwallayenta.

Yanzu Everton na da maki takwas a wasanni hudu da ta buga ta kuma shiga zagayen 'yan 32.

Wasu daga cikin sakamakon wasannin da aka buga a gasar ta Europa a yau na nuna cewa Borussia Monchengladbach ta doke Apollon Limasol da ci 2-0, FC Zurich ta lallasa Villareal da ci 3-2, Tottenham ta doke Asteras Tripolis da ci 2-1.

Haka kuma Inter Milan da St. Etienne sun tashi da ci 1-1 yayin da Sevilla ta doke Standard Liege da ci 3-1.