INEC za ta fara raba katin zabe

Nigeria Hakkin mallakar hoto b
Image caption Katin za a bayar da shi ne a matsayin na dun-dundun

A gobe Juma'a ake sa ran hukumar zaben Najeria mai zaman kanta INEC za ta fara raba katin zabe na dun-dundun a wasu jihohin kasar.

A baya dai hukumar ta shirya raba katunan ne a jihohi 13, amma a yanzu hukumar ta ce za a bayar da su ne a karshen makon nan a wasu jihohi biyar.

Sannan za kuma fara bayarwa a wasu jihohi biyar a ranar 28 ga watan nan na Nuwamba.

Daga cikin jihohin da aka kebe za a bayar a ranakun da aka diba akwai jihar Kano da Adamawa da Imo da Lagos da Nasarawa da Plateau da Rivers da dai sauransu.