'Ana zargin sojoji da kisan kai a Potiskum'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu jihohin arewa maso gabashin Nigeria na karkashin dokar ta-baci

Ana zargin sojojin Nigeria da kashe wasu mutane 16 da suka kama yankin Dogo Tebo na garin Potiskum da ke jihar Yobe.

Al'ummar yankin, sun ga gawawwakin mutanen wadanda ke da alamun harbin bindiga a babban asibiti na Potiskum 'yan sa'o'i bayan da sojoji su kama su lokacin suna dawowa daga Masallaci.

Wani mazaunin Potiskum ya shaidawa BBC cewar sun je asibiti sun ga gawawwakin.

Wani ma'aikacin asibiti a Potiskum ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "sojoji ne suka kawo gawawwarkin kuma duk akwai alamun harbin bindiga a jikinsu."

A ranar Litinin an kashe a kalla mutane 15 sannan wasu 50 suka samu raunuka bayan da aka kaddamar da hari a kan 'yan shi'a da ke muzaharar ashura.

Kawo yanzu babu martani daga rundunar tsaron Nigeria.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama a Nigeria da kasashen waje sun sha zargin dakarun Nigeria da aikata kisan gilla a yaki da Boko Haram tsawon shekaru biyar.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba