Boko Haram: Sojoji sun saki mutane 42

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Sojojin sun baiwa mutane kudi

Jami'an runduna ta bakwai ta sojojin Nigeria da ke jihar Borno sun mika wasu mutane 42 ga gwamantin jihar ta Borno, bayan da aka tantance su cewa ba 'yan kungiyar Boko Haram ba ne.

Kakakin rundunar sojin da ke Maiduguri, Kanal Sani Usman ya ce mutanen da saki an gano cewar ba 'yan ta'adda bane.

Kanal Usman yace "Akwai mutane 42 da aka kama bisa zargin ta'addanci, uku daga cikinsu ba 'yan Nigeria ba ne kuma tuni muka mika wa gwamnatin jihar Borno mutanen domin hade wa da iyalansu."

Ya kara da cewar "Rundunar ta yi wa mutanen dinki sannan ta baiwa kowannensu naira dubu dari."

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin wasu mazauna garin Potiskum a Yobe ke zargin sojojin da kashe wasu mutane goma sha shida da suke zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

An dai sha zargin sojojin Nigeria da aikata kisan gilla amma suna musanta wa.