'Fursunoni fiye da 2,000 sun tsere a Nigeria'

Image caption 'Yan Boko Haram sun yi waon gaba da nakiyoyi daga gidan simiti na ashaka, abin da ke sanya fargabar kara fasa kurkuku

Fursunoni fiye da 2,000 ne suka tsere daga gidajen yari a Nigeria a cikin shekaru biyar din da suka wuce, a cewar jami'ai a kasar.

Mafi yawa daga cikinsu sun tsere ne ta hanyar fasa gidajen yarin da kungiyar Boko Haram ke yi a kasar.

A watan Oktoba kadai, daruruwan fursunoni ne suka tsere, bayan 'yan Boko Haram sun karbe iko da garin Mubi, yayin da a farkon wannan makon ne kuma wasu fursunonin da dama suka tsere daga gidan yari a jihar Kogi.

Kimanin fursunoni 500 ne suka tsere daga kurkuku a birnin Maiduguri a shekarar 2009.

Jimillar fursunoni 2,251 ne suka tsere baki daya kuma mafi yawa daga cikinsu a cewar jami'ai ba a san inda suke ba.

Alkaluman hukumar sa ido a kan gidajen fursuna ta Najeriya sun nuna cewa a watan Yunin da ya gabata akwai fursunoni maza da mata 57,000 a gidajen yari 239.