Kotu ta daure mai daukar nauyin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Da alamu an yi shari'ar tare da yanke hukunci cikin sirri ne

A Najeriya wata babbar kotu da ke jihar Lagos ta yanke hukuncin daurin shekaru goma ga wani mai daukar nauyin Boko Haram a ranar Alhamis.

Saliu Saidu zai yi zaman gidan yarin ne tare da aiki mai tsanani bayan kotun ta same shi da laifi.

Saliu na daga cikin mutane hudu da aka gurfanar a gaban kotun bisa zarginsu da samar da kudade ga kungiyar Boko Haram.

Sai dai kotun ta sallami sauran ukun saboda hukumar SSS da ta shigar da karar ta kasa ba da gamsasshiyar hujja kan zargin da ta ke yi musu.