Wane shugaban kasa ne ya fi kowa talauci?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr. Mujica ya ce zai yi amfani da kudin ne wajen samar da gidaje ga wadanda basu da matsugunai

An yi wa shugaban kasar Uruguay, Jose Mujica, tayin sayen motarsa kirar Volkswagen Beetle a kan kudi dala miliyan daya.

Mr. Mujica wanda aka taba yi wa lakabi da "Shugaban kasar da ya fi kowane shugaba talauci" saboda yadda ya ke tafi da rayuwarsa, ya ce wani Balarabe ne ya yi masa tayin.

Ya kuma shaida wa wata mujallar kasar cewa idan har ya karbi kudaden to zai yi amfani da su ne wajen taimaka wa talakawa.

Shi dai shugaba Mujica wanda aka fi sani da Pepe yana zaune ne a wata sukurkutacciyar gona, kuma yana kyautar da kaso mafi yawa daga cikin albashinsa.

Hakkin mallakar hoto AFP

A shekarar 2010 ne ya bayyana dukiyarsa ta shekarar $1,800 wato daidai kudin da ya sayi motarsa Beetle a shekarar 1987.

Mr. Mujica mai shekaru 79 a duniya ya gaya wa mujallar Busqueda cewa "Tayin ya ban mamaki, kuma da farko ban dauke shi da wani muhimmanci ba, amma daga baya sai aka kara yi mini wani tayin, abin da ya sa na fara daukar batun da dan muhimmanci kenan."

A wajen wani taro na kasa da kasa ne da aka yi a birnin Santa Cruz na kasar Bolivia aka fara yi wa shugaban tayin sayen motar.

Shugaban kasar ya ce bai damu da tara motoci ba saboda haka zai yi farin cikin sayar da ita.

"Ai ba don karyarta Manuela ba, da tuni na sayar da Beetle din". Mr. Mujica ya fada cikin raha.