Al Shabaab ta kwace Kudha

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar mayakan Al Shabaab ta kwace wani yanki mai mahimmanci daga sojojin dake yin biyayya ga gwamnatin Kasar Somalia.

Ganau sun ce an kashe akalla mutane 20 a wani mummunan fada da ya barke bayan da Al Shabaab ta kai hari kan yankin Kudha a ranar asabar da safe.

Dakarun dake goyan bayan gwamnati na yiwa yankin barin wuta, wanda yake a kudancin babban birnin Kismayo.

Dakarun tarayyar Afirka da na gwamnati a 'yan watannin nan sun kwace mahimman wurare daga kungiyar Al Shabaab