An cire manhajar gano masu shirin kashe kansu

Samaritans Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamfanin Samaritans sun baiwa wadanda aka muzgunawa hakuri

An cire manhajar nan mai gano masu shirin kashe kansu daga shafin yanar gizo.

Kamfanin Samaritans da ya fara kirkiro da manhajar ya ce cire manhajar ya zama dole saboda mutane suna nuna damuwa kan ta.

Ita dai wannan manhaja an tsara ta ne ta hanyar yadda da za a gane irin kalmomi da za su iya nuna cewa wani yana so ya dauki ransa a shafin intanet.

Sai dai wasu na ganin manhajar za ta sa masu fama da tabin hankali su zama lamarin ya fi shafarsu.

Tuni dai kamfanin na Samaritans ya bayar da hakuri ga duk wani da manhajar ta sa ya shiga wani mawuyacin hali.

"Mun yi shawarar janye wannan manhaja a wannan lokaci saboda mu sake duba lamarin" In ji Darektan kamfanin Joe Ferns.

Ya kara da cewa kamfanin ya lura cewa akwai bayanai da ra'ayoyi da dama da aka yi watsawa akan wannan lamari wanda hakan ya janyo abin damuwa.

" Saboda haka muna bayar da hakuri domin ba mu yi niyyar muzgunawa wani ba." Ferns ya kara da cewa.