'Yan Boko Haram sun kara kama garuruwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun sha kokarin kama garin na Malamfatori

Rahotanni daga Borno, sun ce mayakan Boko Haram sun kama garuruwan Malamfatori da Bulagana na jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Garuruwan biyu na jihar Borno da ke fama da rikicin Boko Haram na kan iyaka ne da Diffa ta Jamhuriyar Nijar.

Rahotannin sun ce masu tayar da kayar bayan sun kwace garuruwan ne bayan fafatawa da sojin Najeriya.

Kuma mutane akalla talatin ne aka kashe a gumurzun, tsakanin farar hula da 'yan kungiyar.

Wani jami'in Nijar da bai amince a bayyana sunansa ba ya gaya wa BBC cewa sojin Najeriya da suka ji rauni a fadan suna Diffa ana yi musu magani bayan da suka tsallaka zuwa can.

Sai dai hukumomin sojin Najeriya da ke Maiduguri, sun ce ba su da wannan labari.

Karin bayani