An kirkiri yanayin fatalwa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An kirkiri yanayin ne a dakin gwaji na kimiyya

Masu binciken kimiyya sun kirkiri yadda za su sa mutane su ji yanayi na cewa a kwai fatalwa a dakin da suke.

Binciken ya samar da yadda za a sa mutum ya ji cewa akwai wani a dakin da yake alhalin babu kowa sai shi.

Masana kimiyyar sun ce sun gano bangaren kwakwalwar dan adam da ke sa mutum ya ji wannan yanayi na gani ko jin fatalwa.

Dr Giulio Rognini daga cibiyar fasaha ta Switzerland, ya ce,''jin wannan yanayi abu ne da yake a zahiri.''

Ya ce wannan abu ne da yake gama-gari ga mutanen da suka shiga wani yanayi mai tsanani.

Yanayi kamar na masu hawan tsaunuka da kuma mutane da sukan sami kansu cikin wani yanayi mai tsanani da ya shafi tunani, da sauransu.

Domin gudanar da bincike, kwararrun, sun duba kwakwalwar mutane 12 da suke da matsalar kawakwalwa, wadanda suka ce suna ganin fatalwa.

Hakkin mallakar hoto European Press Agency

Masu binciken sun gano, cewa dukkanin mutanen suna da wata illa ko matsala a bangaren kwakwalwarsu da ke sa su san abin da ke kusa da su ko sanin su kansu da kansu, da motsi da kuma inda jiki ya ke.

A karin gwajin da suka yi masanan sun yi gwaji akan mutane 48 masu lafiya, wadanda ba su taba samun kansu cikin wani yanayi na tunani na daban ba.

Masanan sun shirya wani gwaji da ya jirkita yanayinsu zuwa kamar na wadanda suke da matsala a wannan sashe na kwakwalwarsu.

Wadanda a ka gudanar da gwajin da ya hada da rufe musu ido sun ce sun ji wani yana yi na daban, na jin alamun fatalwa ko wata halitta a inda suke.

Masanan sun yi imanin cewa idan mutane suka ji yanayi na ganin fatalwa, kwakwalwarsu ce ke rikicewa, ta ba su lissafin da ba haka yake ba game da inda jikinsu yake, kuma ta sa su ji jikin na wani ne.