Miyagu ne suka kashe dalibai a Mexico

Zanga-zangar dalibai a Mexico Hakkin mallakar hoto
Image caption Zanga-zangar dalibai a Mexico

Gwamnatin kasar Mexico ta ce akwai hujjar dake nuna cewa masu aikata manyan laifuka ne suka kashe daliban nan da suka bata makwanni shida da suka gabata a garin Iguala.

Babban Attorney Janar din kasar Jesus Murillo ya ce uku daga mambobin kungiyar nan ta Guerreros Unidos, sun amsa cewa su suka kashe daliban, sun kuma kona gawarwakin bayan da suka kashe su.

Rahotanni na nuna cewa 'yan sandan yankin Iguala ne suka mika daliban ga 'yan kungiyar, bayan da suka yi wata arangama da su.

Karin bayani