Boko Haram: Soji sun saki mutane 125

Hukumomin sojin Najeriya sun ce sun saki karin wasu mutane 125 a jihar Borno, wadanda aka kama a zargin cewa 'yan Boko Haram ne.

Wannan ne karo na biyu cikin 'yan kwanakin nan da sojojin suka yi hakan.

Mutanen na daga cikin mutane 154 ne da sojojin suka kama a ranar 23 ga watan Satumba a garin Biu dake kudancin Borno.

Jami'an sojin sun ce sun mika wa hukuma wasu mutane 29 da ake tuhuma da laifuka domin su fuskanci shari'ah.

Kanar Sani Usman mukaddashin daraktan hulda da jama'a na runduna ta bakwai ta sojojin Najeriya wanda keda hedikwata a Maiduguri, ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa wadanda aka kama din sun saje ne cikin masu kai dabbobi a manyan motoci zuwa kudancin Najeriya.

Kungiyar ta Boko Haram din dai yanzu haka tana rike da yankuna dadama a jihohin Borno da kuma Adamawa da kuma 'yan mata sama da 200 data sace a Chibok a watan Afrilu.

Gwamnatin Najeriyar tace tana iya kokarinta wajen tabbatar da tsaro a kasar