Ana cece- kuce kan binciken lafiyar Suntai

Image caption Har yanzu Gwamna Danbaba Suntai bai koma kujerarsa ba

A Najeriya, rigimar siyasa a Jihar Taraba ta dauki sabon salo bayan hukuncin da kotu ta yanke game da binciken lafiyar Gwamnan jihar, Danbaba Suntai.

Rahotanni sun ce kotun ta dakatar da aikin kwamitin binciken lafiyar ne, wanda majalisar dokokin jihar ta kafa a cikin watan Satumba.

Magoya bayan Gwamnan sun yi marhaban da hukuncin.

To sai dai majalisar ta ce kotun ba ta hana kwamitin tantance lafiyar gwamnan ba, saboda haka zai ci gaba da aikinsa.