Sudan ta Kudu: An bai wa masu rikici wa'adi

Hakkin mallakar hoto AFP

An bai wa bangarorin da ke fada da juna a Sudan ta Kudu wa'adin makonni biyu da su tsaida magana akan yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma, ko kuma su fuskanci takunkumi daga kungiyar cigaban kasashen gabashin Afrika ta IGAD.

IGAD din tace yanzu bangaren gwamnati da na 'yan tawaye sun amince su kwance damara ba tare da bata lokaci ba.

Ta kuma yi kashedin cewa zata dauki mataki idan wani bangare ya keta wannan yarjejeniyar.

Wani wakilin BBC ya ce ana zargin bangarorin biyu da keta yarjejeniyar da aka cimma a watan Janairu.