An kashe mutane 8 a rikicin Wukari

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga jihar Taraba a arewacin Najeriya na cewa an kashe akalla mutane takwas, aka kuma jikkita wasu da dama, a wani sabon tashin hankali da ya barke a garin Wukari.

Tarzomar dai ta barke ne tsakanin matasan Hausawa da Fulani, a bangare guda, da kuma matasan Jukunawa, a dayan bangaren.

Bayanai na cewa yanzu kura ta lafa yayin da jami'an tsaro, wadan da suka hada har da sojoji, ke sintiri a garin.

Baya ga asarar rayuka da raunukan da wasu suka samu an kuma kona gine-gine.

Hausawa da Fulani dai na zargin 'yan kabilar Jukun ne da kashe wani dansu da aka aika sayen zaren dinkin keke, kana suka ki bada gawarsa.

Daya daga cikin shugabannin Hausawa da Fulani a Wukarin, Audu Ali, ya ce an kashe mutane akalla biyar daga bangarensu.

To sai dai 'yan kabilar Jukun sun musanta zargin soma kisan, inda shugaban matasansu, Mista Zando Hoku, ya ce, kodayake ya ji labarin kashe Bahaushen, ba shi da tabbacin lamarin.

Ya kuma kara da cewa tun ranar Alhamis ne aka shiga zaman dar-dar a garin bayan kashe wani Bajukuni mahayin babur, kuma suna zargin Hauasawa ne da kashe shi.

Ya ce, duk da kokarin da shugabannin al'ummomi suka yi na kwantar da hankulan jama'a, lamarin ya faskara, inda tarzomar ta ta'azzara a ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraban, Joseph Kwaji, ya ce jami'an tsaro sun shawo kan rikicin.

Karin bayani