Nukiliya: Iran da Amurka sun soma tattaunawa

Hakkin mallakar hoto AFP

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya soma tattaunawa akan shirin Nukiliyar kasar sa da sakatren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da kuma babbar mai shiga tsakanin Tarayyar Turai, Catherine Asthon.

Suna so ne su tsaida magana akan yarjejeniyar da suka cimma da zata fara aiki nan gaba a wannan watan.

Wata wakiliyar BBC a Oman, inda ake taron, ta ce ana saran Iran zata amince ta rage yawan Uraniunm dinda take tacewa, domin ayi mata sassauci a takunkumin da aka sanya mata.