An mai da wa Sarki Sanusi II Fasfonsa

Image caption A baya an sami takun- saka tsakanin Sarkin Kano da Shugaban Kasa

Hukumar tsaro ta farin kaya SSS a Nigeria ta maida wa Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanuni II fasfonsa bayan da aka kwace masa a watan Mayu.

Wani jami'in gwamnatin Jahar Kano mai lura da harkokin da suka shafi masarautar Kano Alhaji Tijjani Mailafiya shi ne ya tattabarwa da BBC cewa an maida wa Sarkin takaddunsa na tafiye- tafiye.

A watan Mayu ne dai jami'an hukumar tsaron farin kaya wato SSS suka kwacewa Sarkin na yanzu fasfonsa a lokacin da yake shirin tafiya zuwa kasa mai tsarki wato Saudi Arabiya, bayan takun- sakar da ta shiga tsakaninsa da Shugaban Kasa a wancan lokacin.

A karshen watan Oktoba ne kuma Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II da wasu 'yan majalisar sa suka kaiwa Shugaba Goodluck Jonathan ziyara a fadarsa.