An yi bikin mutanen da suka sauya jinsi

Hakkin mallakar hoto focus bangla
Image caption Bangladesh ta amince da mazan da suka koma mata su bayyana matsayinsu a Fasfo da sauran takardun shaida

An yi biki na kwanaki uku na mutanen da suka sauya halittarsu zuwa mata a birnin Dhaka na kasar Bangladesh.

Mataimaki na musamman ga Firai Ministan kasar ne ya yi jawabi ga mutanen da suka yi fareti, sanye da Sari kuma suna neman a basu 'yanci daidai da kowa.

Bikin dai ya zo ne shekara guda bayan majalisar ministocin kasar ta amince da irin wadannan mutane, a matsayin jinsi na uku.

Sai dai mutanen da kuma masu goyon bayansu sun ce ba a kafa dokar da za ta basu 'yanci daya da kowa ba.