'Yan jihadi a Masar sun yi mubaya'a ga IS

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan IS na da'awar kafa daukar musulunci

A wani sakon da ta saka a shafinta na Twitter, babbar kungiyar masu jihadi a kasar Masar ta ce ta yi mubaya'a ga kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci.

A sakon mai mintoci tara, kungiyar Ansar Beit al-Maqdis na cewa, za ta mika wuya, tare da kuma yin ladab ga shugaban kungiyar ta IS Abu Bakr al-Baghdadi.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ta kasar Masar ya ce wannan sanarwa, ba za ta yi wani tasiri kan martanin gwamnati kan kungiyar da ta yi alwashin rusawa ba.

Karin bayani