Nukiliya: An kasa cimma nasara kan Iran

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Iran ta kafe cewa ita shirinta ba na hada makamin kare dangi bane, amma kasashen Yamma na shakku

An kammala tattaunawar kwanaki biyu tsakanin Iran da Amurka da Tarayyar Turai ba tare da an cimma nasara ba akan yarjejeniyar shirin nukiliya na Iran.

Wani jami'in Iran din ya ce an samu dan cigaba, yayin da su kuma Amurkawa suka yi gum da bakinsu.

Bangarorin dai sun gana ne a Oman makwanni biyu kafin karewar wa'adin mako biyu da aka diba domin cimma yarjejeniyar hana Iran kera makaman kare dangin.

Manyan jami'an bangarorin da ke tattaunawar sun rika yin takatsantsan a martaninsu yayin da suka fara zaman karshen wanda aka yi shi ba a bainar jama'a ba.

Kasashen Yammacin duniya su na son ganin Iran ba ta samu damar kera makamin kare dangi ne ba.

Amma sun ce za su iya yarda da shirinta na inganta Uranium na wani takaitaccen mataki da za ta iya samar da makamashi da sauran ayyuka na zaman lafiya.