Bam ya hallaka mutane 47 a Potiskum

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An garzaya da mutane 79 zuwa asibiti bayan da suka samun raunuka

Wani daga cikin 'yanuwan mutane 47 da wani dan harin kunar bakin wake ya hallaka a wata makarantar sakandare dake garin Potiskum a jihar Yobe arewa maso gabashin Najeriya, ya soki lamirin gwamnati na rashin daukar matakan tsaro a yankin.

Ya ce dole sai gwamnati ta maida hankali wajen fadan da take yi da kungiyar Boko Haram, yayinda matsalar ke kara kazancewa.

Tun farko dai 'yan sanda a Nijeriyar sun ce dan harin kunar bakin waken ya hallaka mutane akalla 47, yayinda wasu mutanen 79 suka samu raunuka kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda kasar Emmanuel Ojukwu ya shaidawa BBC.

Wani mutum da ya rasa kaninsa a harin ya shaida wa BBC cewar "Kanina dalibi ne a makarantar. Shekarunsa 16 ne mun yi jana'izarsa. Bam din ya cire masa kafa."

Ya kuma bukaci gwamnati ta maida hankali wajen kare rayukan al'ummar kasar.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan wani dan kunar bakin wake ya kashe 'yan Shi'a 21 masu muzaharar Ashura a garin na Potiskum.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin amma ana zargin kungiyar Boko Haram.