Potiskum: Jonathan ya nuna alhini

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane da dama sun jikkata

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwansu sakamakon harin bam a wata makaranta a Potiskum.

Wani dan kunar bakin wake da ya saje da dalibai ne ya tayar da bam a cikin wata makaranta, lamarin da ya hallaka mutane 47, sannan kuma wasu 79 sun samu raunuka.

Sanarwar fadar shugaban Nigeriar ta ce, duk da koma bayan da ake samu, gwamnatin kasar ta lashi takobin samun nasara a kan 'yan ta'adda.

Sai wani mutum da ya rasa kaninsa a harin da aka kai Potiskum, ya soki gwamnati inda ya bukace ta tashi tsaye saboda lamarin ya na nema ya fi karfin gwamnatin.

Ana zargin kungiyar Boko Haram dai kai wannan harin, musamman saboda adawarta da karatun Boko.