An sace kanin Nuhu Ribadu a Yola

Image caption Kawo yanzu Malam Nuhu Ribadu bai ce komai ba a bainar jama'a

'Yan bindiga a Nigeria da ba a san ko su waye ba sun sace kanin tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu.

Wani makusancin Nuhu Ribadu ya tabbatarwa da BBC cewar a ranar Lahadi da yamma aka sace Malam Sani Ribadu a gonarsa da ke wajen garin Yola babban birnin jihar Adamawa.

Kawo yanzu babu bayanai game da inda 'yan bindigar suka kai Sani Ribadu amma kuma ana alakanta sace shi da siyasa kasancewar shi tsohon shugaban karamar hukuma ne kuma tsohon dan majalisar dokoki ne.

Sace mutane domin kudin fansa na da cikin ayyukan miyagun mutane a Nigeria da ake samun kudade masu yawa.