'Yan arewa sun nuna damuwa kan tsaro

Taswirar Nigeria
Image caption Wasu na zargin 'yan arewar da rashin yin katabus wajen magance matsalolin yankin

A Najeriya, wasu 'yan arewacin kasar na nuna damuwa a bisa halin tabarbarewar tsaron da yankin ke ciki.

Inda dattawan ke ganin ya kamata a hada kai don ceto yankin daga matsalolin rashin tsaron da ya shiga.

Sun bayyana hakan ne yayin bikin bude wani sabon ofishin gidauniyar Ahmadu Bello a Kaduna.

Kashe-kashen rayukan al'umma da yawaitar hare-haren kungiyar Boko Haram na daga cikin abubuwan da ke ci wa 'yan arewacin Najeriyar tuwo a kwarya.