Kamaru ta kashe 'yan Boko Haram 1000

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya-bayan nan an fafata a garin Malam Fatori da ke bakin iyakar Kamaru da Najeriya

Hukumomi a jamhuriyar Kamaru sun ce kasar ta kashe 'yan Boko Haram fiye da 1000 a cikin watanni shidan da suka wuce.

Yayin da a bangarenta kuma jami'an tsaron kasar 33 ne suka rasa rayukansu a tsawon wannan lokaci.

kakakin ma'aikatar tsaron kasar ya ce Kamaru za ta ci gaba da jan daga domin kare kasa da kuma jama'arta, abin da yasa aka kara aika wasu sabbin jami'an tsaron.

An sha fafata kazamin fada tsakanin dakarun Kamaru da kuma 'yan Boko Haram a bakin iyakar kasar Kamaru da Najeriyar.