An kashe mutane a Congo

Hakkin mallakar hoto
Image caption An caccaki a dakarun majalisar dinkin duniya

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun tabbatarwa da BBC cewa ba za su iya kare rayukan daukacin fareren hula ba.

Mutane akalla dari da ashirin ne aka hallaka a yankin Beni da ke kusa da kan iyakar kasar Uganda tun daga farkon watan Oktoba.

An kuma zargi kungiyar 'yan tawayen kasar Uganda da aikata kashe-kashen.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bata da isassun kayan aikin da za ta aike da dakaru zuwa ko wane kauye dake fuskantar barazana.

Matasan yankin dai sun kafa kungiyoyi don kare kansu, ana kuma kara sukar Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnati kan rashin basu kariya.