Kungiyoyi sun soki takarar Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Jonathan da saba alkawari kan yarjejeniyar karba-karba

A Najeriya wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama da na addini sun yi suka kan bikin bayyana aniyar takara na shugaba Goodluck Jonathan bayan kisan dalibai a Yobe.

Kungiyoyin na ganin bai kamata shugaban ya kaddamar da aniyarsa, kwana daya bayan dalibai 47 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a makarantarsu da ke Potiskum.

Haka kuma suna ganin rashin dacewar bikin ganin yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa da yankun a arewa-maso gabashin kasar.

Hakan na zuwa yayin da manyan jaridun kasar hankalinsu ya karkata kan tallar bikin kaddamarwar Shugaba Jonathan, maimakon labarin kashe daliban na Yoben.