An yanke wa matukin jirgin ruwa hukunci

Image caption Iyalan wadanda suka mutu sun soki hukuncin

An yanke wa matukin jirgin ruwan na kasar Koriya ta Kudu hukuncin daurin shekaru 36 a gidan yari.

An samu Lee Joon-Seok da laifin sakaci, to amma an wanke shi da laifin kisan kai.

Jirgin ruwan da ya nutse a cikin watan Afrilu ya halaka mutane fiye da 300.

Ya amince a kotun cewar zai karashe sauran rayuwarsa a gidan yari, to amma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sun nuna fushinsu da cewar ba a same shi da laifin kisan kai ba.

Masu gabatar da kara sun ce za su daukaka kara game da wani bangare na hukuncin, hade da samun daya daga cikin ma'aikatan jirgin ruwan da laifin kisan kai, amma ba a samu matukin ba.