An kai hari a garin Maiha na Adamawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mazauna Maiha sun ce an yi ta harbe-harbe

Mazauna kauyukan Maiha na jihar Adamawa a Nigeria sun ce 'yan Boko Haram sun kai musu hari ranar Litinin.

Daya daga cikinsu ya shaidawa BBC cewa maharan sun yi ta harbe-harbe lokacin da suka shiga garin, yana mai cewa sun gaya musu kada su gudu.

A cewarsa, sun tsere ne kan duwatsu, kuma a can za su kwana domin tsira da rayuwarsu.

Mutumin ya kara da cewa babu jami'an tsaro a lokacin da 'yan Boko Haram din suka shiga kauyen na Maiha, yana mai cewa daga nan 'yan bindigar sun nufi hedikwatar karamar hukumar ta Maiha

Karin bayani