Gobara daga karkashin gado a jihar Bauchi

Image caption A 2013 ma wata gobara mai daure kai a garin Misau na jihar ta Bauchi ta kone gidaje da yawa

Rahotanni daga jihar Bauchi a arewa maso gabashin Nijeriya na cewa wata gobara ta al'ajabi, ta kone gidaje da suka kai 164.

Har yanzu an kasa gano sanadin gobarar da ke ci gaba da ta'adi, musamman a garin Soro na karamar hukumar Ganjuwa ta jihar.

Wani mazaunin garin ya ce "Wutar na kama wa ne daga can cikin daki, kuma daga karkashin gado, akalla gidaje biyar zuwa 20 na kamawa a yini."

Inda ya bayyana cewa wani lokacin kuma wutar na kamawa ne daga cikin rufin daki, kuma a wasu lokuta gida kan kone kurmus, sai dai kawo yanzu babu asarar rayuka.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi ta tabbatar da lamarin, wanda ita ma ta ce yana da daure kai amma kuma tana bincike kan abin da ke haddasa wutar.