APC ta yi raddi kan takarar Jonathan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption APC na da 'yan takarar shugaban kasa hudu, abin da yasa wasu ke ganin za a iya samun rarrabuwar kawuna

Jam'iyyar adawa mafi girma a Najeriya, APC ta ce za ta bi hanya ta dimokradiyya wajen fitar da dan takarar shugaban kasa, ba kamar jam'iyya mai mulki ba da babu wanda ya isa ya yi takara da shugaba Goodluck Jonathan kasa.

A wata hira da BBC, mataimakin shugaban jam'iyyar shiyyar arewacin kasar, Sanata Lawal Shu'aibu ya ce kaddamar da takarar shugaban kasar bai zo musu da mamaki ba.

Haka kuma ya kara da cewa tun da aka yi Najeriya ba a taba samun lokacin da kasar ke cikin matsanancin talauci ba kamar lokacin mulkin Jonathan.

Sanata Lawan ya kuma kara nuni da mawuyacin halin rashin tsaro da arewacin kasar ke fuskanta, abin da yasa yake ganin shugaba Jonathan bai yi wani abin azo a gani ba na inganta rayuwar talakan Najeriya.

A jawabin shugaba Goodluck Jonathan yayin kaddamar da takararsa a ranar Talata, shugaban ya zayyana jerin muhimman abubuwan da ya cimma, ciki har da rage talauci tsakanin al'ummar kasar da bunkasa tattalin arziki.