Amurka da China sun kulla huldar kasuwanci

Shugaba Obama da shugaban China Xi Jinping Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu cikin shekaru 5, albarkacin taron APEC

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce shugaba Obama da shugaban kasar China Xi Jiinping sun yi sabbin alkawaurran rage yawan hayaki mai gurbata muhalli da ake fitarwa.

A ganawar da shugabannin suka yi a birnin Beijin shugaba Obama ya ayyana wani sabon kiyasi na rage yawan hayaki mai gurbata muhallin da za a rage da kashi 27 cikin 100 a shekarar 2025 kwatankwacin yanayin da ake da shi a 2005.

Shugaba Obaman ya kara da cewa shi da shugaba Xi sun amince da muhimmancin kara kasuwancin da za su bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, da samar da ayyukan yi ,idan Amurka ta kara yawan kayan da take shigarwa China hakan na nufin wata karin dama ga kasuwancin Amurka.

Duk da cewar shugaba XI bai ayyana wani kiyasi na yawan hayakin da za a rage ba, yace China za ta kayyade yawan hayaki mai gurbata muhallin da take fitarwa nan da shekarar 2030 ko kafin lokacin.

Wannan sanarwa na zuwa ne ya yin da shugabannin biyu Sukai karin wasu tattaunawa, bayan wani cin abincin dare da suka yi a jiya talata a karshen taron kasashen yankin Asia Pasific.

A bangare guda kuma ana saran hamayyar kasuwanci za ta fito fili tsakanin Amurka da kuma China.