'Yar kunar bakin wake ta kai hari Kontagora

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani dan kunar bakin wake ya kashe dalibai 47 a wata makaranta a garin Potiskum na jihar Yobe ranar Litinin

Rahotanni daga garin Kontagora na jihar Niger na cewa an kai hari a wata makarantar horar da malamai da ke garin.

Wasu malamai a kwalejin horar da malamai sun tabbatar wa da BBC cewa wata 'yar kunar bakin wake ce ta tayar da bam din.

Bayanai sun nuna cewa matar ta yi kokarin shiga ajin da ake koyar da dalibai sai dai ba ta yi nasara ba kuma bam din ya fashe.

Ita kadai ce dai ta mutu a harin, yayin da wasu mutane bakwai kuma suka samu raunuka, kuma a yanzu haka suna samun kulawa a asibiti.

Kawo yanzu babu wani bayani daga jami'an tsaro ko hukumomi a kasar game da harin na ranar Laraba.