Ana shirin taimaka wa Kamaru yaki da Boko Haram

Kwamitin Sulhu Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kwamitin Sulhu

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da yankin kasashen Afrika ta tsakiya ta ce za ta bukaci da kwamitin sulhu ya agaza wa Kamaru wurin yaki da kungiyar Boko Haram.

A cikin sanarwar da kakakin babban sakataren majalisar dinkin duniya Abdoulaye Bathily ya fitar, ya ce a baya-bayan nan 'yan kungiyar Boko Haram na kara yawan hare-hare a lardin arewa mai nisa na Kamaru, abin da ke haddasa asarar rayuka da garkuwa da jama'a.

A kwanaki baya ne Kamarun ta bada sanarwar cewa adadin 'yan Boko Haram da ta kashe a baya bayan nan zasu kai dubu daya.

Akwai dubban 'yan gudun hijirar Nijeriya a kasar ta Kamaru da suka tsere wa rikicin Boko Haram .