Birtaniya za ta kafa sabuwar doka kan ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Cameron ya bayyana sabon matakinne a Australia

Firayi Ministan Birtaniya David Cameron ya ba da cikakken bayani game da dokar da ake shirin kafawa ta yaki da ta'addanci.

Dokar za ta kawo karshen samun 'yan Birtaniya masu kaifin ra'ayi da ke zuwa Syria da Iraki suna shiga yaki.

'Yan sanda za su samu karin iko na kwace fasfo na mutanen da ake ganin alamar suna da niyyar fita daga Birtaniya ne don mara baya ga kungiyar masu yunkurin kafa kasar Musuluncin.

Har ila yau kuma za a dauki matakai na wani takaitaccen lokaci na hana 'yan Birtaniya komawa kasar bayan sun marawa ayyukan ta'addanci baya.

Bugu da kari kuma, kamfanonin jiragen sama za su fuskanci tara mai tsanani idan suka gaza daukar karin matakai na binciken sunayen fasinjojinsu.