An gano tulin makamai a arewacin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun addabi al'ummar arewacin Kamaru

Wasu rahotanni da ba na hukuma ba sun ce an gano wasu makamai a cikin wasu motoci a yankin arewacin Kamaru a wurare daban-daban.

Kawo yanzu babu bayanai daga inda makaman suka fito amma ana zargin cewa za a nufi kasar Chadi ne da su ne .

A baya-bayanan dai hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suna ta rubanya a wasu garuruwa na arewacin Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta ce a cikin watanni shida ta hallaka 'yan Boko Haram kusan 1,000 a yayinda ta rasa dakarunta 33.

A kan haka ne Kamarun ta aika karin jami'an tsaro filin daga domin fafatawa da 'yan Boko Haram.