Ebola: An dage dokar ta baci a Liberia

liberia ebola Hakkin mallakar hoto epa

Shugabar kasar Liberiya, Ellen Johnson Sirleaf ta dage dokar-ta-bacin da aka saka a kasar domin dakile yaduwar cutar Ebola.

A wani jawabi da ta yi wa 'yan kasar, Shugabar ta ce wannan mataki da aka dauka na cire dokar ba yana nufin cewa an kammala yaki da cutar ba ne.

Sai dai ta ce hakan na nuna irin ci gaban da kasar ta samu ne wajen rage cutar, inda ta kara yin kira ga 'yan kasar da su kara himmatuwa wajen ganin kasar ta shawo kan cutar ta Ebola.

Ta ce "Laberiya ba za ta taba zama kasar da ta shawo cutar Ebola ba har sai makwabtanmu sun magance wannan cutar, hakan kuma na nufin ba za mu yi sakaci wajen yaki da cutar ba muddin muna so mu shawo kanta."

Adadin masu kamuwa da cutar ta Ebola dai tana cigaba da karuwa a kasashen da ke makwabtaka da Liberiyar, wato Guinea da Saliyo.