WHO ta damu da karuwar Ebola a Mali

Cutar Ebola a Mali
Image caption Cutar Ebola a Mali

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta damu da karuwar masu kamuwa da cutar Ebola kasar Mali bayan mutuwar mutum na uku.

Hukumar ta ce har yanzu adadin mutanen da ke kamuwa da cutar na karuwa a makwabciyar kasar Mali wato Saliyo.

Kawo yanzu dai cutar a cewar hukumar ta kashe mutane 5160 a yankin Yammacin Afrika.

Ko da ya ke hukumar tace adadin mutanen da ke mutuwa yana raguwa yanzu a Guinea da Liberia abin da ya sa hukumar ta yi amanna cewar yakin da ake yi da cutar na yin tasiri.

Karin bayani