'Yan Majalisa sun gana da manyan hafoshin tsaro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Babban hafsan dakarun Nigeria, Air Marshal Alex Badeh

Manyan hafsoshin tsaron Nigeria sun yi wa 'yan majalisar dattijai bayanai kan matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar.

'Yan majalisar dattawan kasar ne suka kira hafsoshin tsaron sakamakon yadda sojojin kasar suka kasa murkushe mayakan Boko Haram kamar yadda suka yi wa majalisar alkawari watanni shida da suka wuce.

'Yan Nigeria na sukar dakarun kasar a yakin da suke yi da Boko Haram gannin cewar kawo yanzu an kasa samu galaba a kansu.

Rikicin Boko Haram ya janyo hasarar rayukan mutane da dama a yayinda 'yan kungiyar ke ci gaba da kwace yankunan kasar.