Shell ya boye girman malalar mai a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsalar tsiyayar man a Ogoni ya gurbata ruwan sha

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce kamfanin hako mai na Shell ya boye girman barnar da malalar mai ya yi a Najeriya.

Amnesty ta ce wasu takardun kotu ne suka fallasa cogen da kamfanin ya yi kan wasu manyan malalar mai biyu da ya faru a kasar, domin kada ya biya diyya mai yawa.

Bayanan kotun sun nuna cewa an ankarar da Shell cewa wani bututunsa ya cinye shekarun nagartarsa, kafin ya tsiyayar da gangan mai rabin miliyan.

Katafaren Kamfanin ya shaida wa BBC cewa ba gaskiya bane cewa yana sane bututun nasa ya lalace, amma ya cigaba da amfani da shi.

A wani sabon rahoton da ta fitar Amnesty ta ce manyan matsalolin tsiyayar mai a Bodo da yankin Ogoni a kudancin Najeriya a 2008, sun shafi yanki mai fadin kilometa 90.