Amurka ta yi wa Nigeria raddi kan makamai

Hakkin mallakar hoto
Image caption Amurka ta ce kalaman da Nigeria ta yi game da sayar da makamai soki-burutsu ne

Gwamnatin Amurka ta ce tana taimakawa Nigeria sosai game da yaki da ta'addanci don haka maganar da Nigeriar ta yi cewa ba a sayar mata makamai ba soki-burutsu ne.

Wata jami'ar gwamnatin Amurka ta ce kasarta ta taimaka wa sojin Nigeria da bayanan sirri da horas da sabuwar bataliyar sojin kasar da kuma gudanar da cikakkiyar tattaunawa kan yadda za a tunkarin matsalar Boko Haram, tun lokacin da aka sace 'yan matan Chibok watanni shida da suka gabata.

Ranar Talata ne dai jakadan Nigeria a Amurka, Adebowale Adefuye, ya soki Amurka saboda kin sayarwa kasarsa makamai domin yaki da Boko Haram.

Amma kakakin gwamnatin Amurka, Jen Psaki, ta ce Amurka ta bayar da umarnin sayar da kayan yaki ga sojin Nigeria, kodayake ta amince cewa Amurkan ta ki sayarwa jiragen saman yaki masu saukar ungulu ga sojin na Nigeria saboda ba ta da tabbacin sojin za su iya yin amfani da su.

Karin bayani