Ba bu tabbacin kariyar sirrin mu - Amurkawa

Edward Snoden tsohon jami'in leken asiri na Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Edward Snoden tsohon jami'in leken asiri na Amurka

Wani sabon bincike ya nuna cewar Amurkawa ba su da tabbaci a kan matakai na kariyar sirrin su.

A cewar binciken, mafi rinjaye, kashi 91 cikin dari na Amurkawa masu mu'amalla da kamfanoni ba su da iko a kan bayanan su na sirri da ake samu da kuma yadda kamfanonin ke amfani da su.

Binciken na kamfanin Pew ya kuma nuna cewar karin wasu kashi 80 suna jin cewa kamata ya yi a nuna damuwa da leken asiri na gwamnati.

Kamfanin ya yi nazarin halayyar su a kan sirri da bayanai a zargin da Edward Snowden ya yi game da leken asiri na gwamnati.

Wani kwararre ya bayyana sakamakon binciken a matsayin wani abu da bayar da mamaki ba.

Marubuciyar sakamakon binciken Mary Madden ta bayyana cewar hankalin da kafofin watsa labarai suka ba zargin da Snowden ya yi da leken asirin mutane da dama tsakanin hukumomin bincike na Amurka na nufin mutane da dama suna nuna damuwa da kariyar sirrin su.

Tace, "akwai matukar damuwa dangane da leken sirrin da gwamnati ke yi tsakanin Amurkawa da kuma rashin imanin da suke da shi a kan fannonin sadarwa kan sha'anin tsaro.

Bugu da kari kuma, mutane da dama suna da ra'ayi daya a kan yadda masu mu'amalla da kamfanoni ba su da iko da yadda kamfanonin ke tattara bayanansu na sirri da kuma yadda suke amfani da su.

Tun lokacinda tsohon ma'aikacin hukumar leken asirin ta Amurka Edward Snowden ya fara fallasa ayyukan leken asiri na hukumar leken asiri ta kasa ta Amurka da kuma na hukumar leken asiri ta Brittaniya, kamfanoni sun rinka tabbatar ma abokan huddar su cewar ba bu abinda zai taba bayanasu na sirri.

Wasu kamfanonin da suka hada da Microsoft da Yahoo da Google sun yi alkawarin bayar da kariya ga bayanan sirri na mutane ta yadda babu yadda za a yi gwamnati ta yi musu kutse.

Binciken ya nuna cewar yawancin masu mu'amalla da kamfanoni ba su gamsu da irin kariyar da kamfanoni ke baiwa bayanan su na sirrin ba.

Karin bayani